1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kaddamar da kunshin farfado da tattalin arziki a Jamus

Zulaiha Abubakar
June 4, 2020

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta sanar da amincewa kan fidda wani kunshi da zai farfado da tattalin arziki daga annobar coronavirus.

https://p.dw.com/p/3dEDS
Deutschland Berlin | Pressekonferenz | Angela Merkel
Hoto: Getty Images/Pool

Kudaden da yawansu ya kai euro biliyan 130 gwamnatin ta ware don rage radadin da annobar da haifarwa al'ummar kasar tare da ragewa iyalai haraji da kuma karin Euro 300 cikin kudaden da Jamus ke biyan kowanne yaro karami da kuma karin tallafin gwamnati a cinikin motoci masu amfani da wutar latirisha.

Sanarwar ta kara da bayyana yadda gwamnatin Jamus ta kebe wasu Euro biliyon 50 domin tunkarar kalubalen sauyin yanayi da sanya fasahar kimiyya cikin gudanar da harkokin tattalin arzikin kasar, wadannan matakai sun samu amincewar jam'iyyun CDU da CSU da kuma SPD bayan shafe awanni 21 ana tattaunawa.

Shugabar gwamnati Angela Merkel ta kara da cewar mambobin gwamnatin hadaka sun amince da wannan sabon shiri da zai saukakawa al'ummar kasar matsin da annobar COVID-19 ta haifar.