Jamus tace akwai sake a game da rahoton da Eu ta fitar | Labarai | DW | 08.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus tace akwai sake a game da rahoton da Eu ta fitar

Gwamnatin Jamus ta soki lamirin wani rahoto da kungiyyar Eu ta fitar dake nuni da cewa akwai sa hannun kasar, wajen yadda Amurka take jigilar mutanen da ake zargi yan ta´adda ne izuwa gidajen kurkuku na sirri.

A cewar kakakin gwamnatin na Jamus, akwai bukatar majalisar kungiyyar hadin kann turai ta sake nazari a game da wannan rahoto.

Rahoton wanda kungiyyar kare hakkin bil adama ta kungiyyar ta Eu ta fitar, ta kuma soki lamirin wasu kasashe 13 na kasashen turai da taimakawa hukumar CIA ta Amurka wajen gudanar da wannan mummunan aiki.

Rahoton na kungiyyar kare hakkin bil adama na kungiyyar ta Eu da dan majalisa daga kasar Swiss, Mr Dick Marty ya gabatar a jiya laraba tuni Amurka tace akwai kura kurai da yawa a cikin sa.