1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta yi gargadi kan kin Yahudawa

Yusuf Bala Nayaya
March 11, 2019

Shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier ya yi kira na a dauki mataki mai tsauri kan masu nuna kyamar Yahudawa a kasar.

https://p.dw.com/p/3ElNK
Deutschland Bundespräsident Steinmeier
Hoto: imago/epd/C. Ditsch

Kasar Faransa ta fitar da rahoto da ke nuni da cewa an samu kari na nuna kyama ga Yuhudawa da kashi 74 cikin dari yayin da a Jamus a shekarar bara aka ga karuwar da kashi sittin cikin dari. A cewar gwamnatin ta Jamus dai an samu karuwar aikata laifuka masu nasaba da kyamar Yahudawa da adadin da ba a ga irinsa ba a tsawon shekaru 10 inda aka samu laifuka 1,646 a shekarar ta 2018.

Shugaba Steinmeier ya yi wannan kalami ne a yayin bude bikin "Makon 'yan uwantaka", wanda ake shiryawa a duk shekara a kasar ta Jamus bikin da ke hade mabiya addinin Kirista da Yahudawan.

Shugaban ya ce sabon tsarin na nuna kyama ga Yahudawa na faruwa ne bayan da aka samu karuwar baki a kasar wadanda asalin kasar da suka fito nuna kyama ga Yahudawa sanannan abu ne.