Jamus ta yaba da matakin Amirka
February 5, 2021Talla
A wani bangare na sake fasalin manufofin kasashen waje da na tsaro da aka gabatar a ranar Alhamis, Biden ya sanar da dakatar da shirye-shiryen wanda ya gada wato tsohon shugaba Donald Trump na rage kasancewar sojojin Amurka a Jamus, ginshikin tsaron NATO tun farkon fara yakin cacar baki.
Ana ganin matakin na tsohuwar gwamantin Shugaba Trump na da nasaba da dangantaka mai tsami tsakaninsa da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da kuma yawan korafin da yake yi na cewa kasasahen Turai da suka fi karfin tattalin arziki na kasashe kudi kalilan kan sha'anin tsaro.