1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta tabbatar da mutunta manufofin Turai

April 22, 2013

Shugaban gwamnatin Jamus ta musanta yin katsalandan da gaba gadi cikin manufofin Kungiyar Tarayyar Turai

https://p.dw.com/p/18KhV
Hoto: DW/R. Romaniec

A wannan Litinin, Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi fatali da maganar cewa kasar ta na gaban kanta wajen daukan matakai bisa abubuwan da suka shafi Kungiyar Kasashen Tarayyar Turai.

Merkel ta ce, Jamus tana tuntubar kasar Faransa da sauran kasashe mambobin kungiyar kan duk wani abu da ya shafi kasashen. Ta ce, wani lokaci saboda Jamus ke kan gaba wajen karfin tattalin arziki shi yasa ake ganin kasar ta zama gagara-badau, amma ba haka batun ya ke ba.

Shugaban gwamnatin ta Jamus tana mayar da martani ne, kan masu sukar rawar da kasar ke takawa wajen magance rikicin tattalin arzikin da wasu kasashen Turai masu amfani da kudin Euro ke fuskanta.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal