Jamus ta na kan gaba wajen samar da fasahar neman bayanan sirri | Zamantakewa | DW | 24.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Jamus ta na kan gaba wajen samar da fasahar neman bayanan sirri

Ana ci gaba da samun bunkasan kasuwar na'urori na zamani da ake amfani da su wajen neman bayanan sirri ta wayar hanu, kan laifuka masu nasaba da ta'adanci.

Ana ci gaba da samun bunkasan kasuwar na'urori na zamani da ake amfani da su wajen neman bayanan sirri ta wayar hanu, kan laifuka kamar ta'adanci. Wannan fasaha daga kasashen Yammacin Duniya ake samu, kuma kasar Jamus ta na kan gaba wajen samar da fasahar.

Kamfanonin kasar Jamus na kan gaba wajen samar da fasahar wadda ake amfani da ita wajen neman bayanan sirri ta wayar hanu da na'ura mai kwakwalwa. A cikin shekara ta 2010 kamfanin Siemens ya samar da irin wannan fasaha ga kamfanin sadarwa na kasar Siriya mai suna Syriatel. Kasashen Libiya da Masar na amfani da irin wannan fasaha wadda ake samu daga kasashen Yammacin Duniya.

Kasar Bahrain ta na amfani da fasahar daga Turai da Amirka wajen duba aiyukan 'yan adawa a cikin kasar. Houssam Aldeen dan jarida da ke Damascus babban birnin kasar Siriya, ya yi aikin soja na shekaru biya da rabi, kuma ya na da masaniya kan yadda ake sarrafa irin wannan na'ura ta binciken sirri. Ya na fassara wa 'yan jaridun kasashen ketere, jami'an tsaron kasar sun cafke shi, tare da zargin cewa ya na sayar da bayanan sirri wa kungiyoyin kasashen duniya. Kua ya tabbatar da masaniya kan yadda ake sarrafa fasahar.

Sukar neman bayanan sirri

Amma akwai masu nuna damuwa bisa yadda kasashen Yammaci ke bayar da fasaha wa gwamnatocin kasashe 'yan kama karya, wadanda ke amfani da fasahar wajen kama masu sukar manufar gwamnatocin. Jan van Aken kwararre kan harkokin irin wannan fasaha ya nuna damuwa, sannan ya kara da cewa haka kasuwanci ya gada.

A matakin kasa da kungiyar kasashen Turai, ba kasafai ake takaita sayar da kayayyaki fasahan binciken sirri ba, kamar yanayin sayar da makamai. Yanzu haka an saka tukunkumin fitar da kayayyaki zuwa Siriya, tare da takaita na Iran, amma a wurare kalilan aka tilas kamfanonin Jamus neman izinin fitar da kayayyaki. Idan ma akwai saboda dalilai na abun da ya dace, amma ba domin dalilai na shari'a ba. Konstantin von Notz mai magana da yawun jam'iyyar the Green kan lamuran cikin gida da hanyar sadarwa ta Internet ya bayyana takaici, bisa yadda babu wani mataki da za a iya dauka na shari'a.

Yanzu bisa halin da ake ciki, kamfanonin Jamus za su ci gaba da sayar da fasaha ta binciken sirri cikin kasashen duniya, saboda babu wani tarnakin da su ke fuskanta.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu