1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta lashe Costa Rica da ci 4 da 2 a wasan farko na gasar cin kofin duniya

June 9, 2006
https://p.dw.com/p/Buuh

Karshen tika dai masu iya magana kan ce wai tik, dazu dazun nan aka fara gasar cin kofin kwallon kafa na duniya na karo 18 a nan Jamus, inda aka yi karawar farko tsakanin Jamus mai masaukin baki da kuma Costa Rica. Da farko shugaban tarayyar Jamus Horst Köhler ya kaddamar da fara wasannin bayan wani kasaitaccen buki da aka yi a babban filin wasan kwallon kafa na birnin Munich.

Shugaba Köhler ke nan lokacin da yake kaddamar da wasan na cvin kofin kwallon kafa inda yayi maraba da dukkan masu sha´awar wasan kwallon kafa wadanda suka hallara a Munich da ma a duniya baki daya. Shugaba Köhler ya kuma yi tuni ga taken wasanni na bana wato Jamus na maraba da bakin ta daga ko-ina cikin duniya.

A karawar farko da aka kammala dazu dazun nan Jamus ta lashe Costa Rica da ci 4 da 2. Da misalin minti 5 da dakika 3 dan wasan Jamus Filip Lahm ya saka kwallo na farko a gasar cin kofin na bana. In an jima ne za´a yi wasa na biyu tsakanin Poland da Ecuador a kasaitaccen filin wasan kwallon kafar nan na birnin Gelsenkirchen.