Jamus ta karfafa amfani da manhajar yaki da corona | Labarai | DW | 20.06.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus ta karfafa amfani da manhajar yaki da corona

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayar da shawarar amfani da damar da aka samu ta sabuwar manhajar da aka kirkiro mai yaki da yaduwar cutar corona tsakanin jama'a.

A wannan makon ne dai aka kaddamar da sabuwar manhajar wadda ake saukewa a wayoyin hannu, kuma manhaja ce mai karfin adana bayanan da ta tattara tare da nuna mai cutar nan take. A cewar Angela Merkel amfani da 'yan kasar Jamus za su yi da sabuwar manhajar, shi ne zai taimaka wajen samar da sakamakon da ake bukata game da cutar don daukar mataki.

Manhajar na kuma iya shaida wa sauran wadanda ke da ita a wayoyinsu, matsayin duk wanda ya gitta kusa da su, masalan idan ya kamu. Gwamnatin Jamus dai ta tsaya kan tabbatar da tsarin manhajar, bai kai ga tattara bayanan sirri na wadanda za su yi amfani da ita ba.