Jamus ta ce ba ta tsammanin masu gadin Erdogan da ake tuhuma za su halarci taron G20 | Labarai | DW | 26.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus ta ce ba ta tsammanin masu gadin Erdogan da ake tuhuma za su halarci taron G20

Ana zargin wasu masu tsaron lafiyar Shugaba Erdogan da cin zarafin masu zanga-zanga lokacin ziyarar da ya kai Washington.

A wannan Litinin Jamus ta ce ba ta sa rai jami'an tsaro da na 'yan sandar Turkiyya da ake zargi da cin zarafin masu zanga-zanga a birnin Washington, za su rako shugaban Turkiyya Tayyip Recep Erdogan zuwa kolin kungiyar kasashen G20 da zai gudana mako mai zuwa a birnin Hamburg na arewacin Jamus.

Bayanin zargin da ake wa wasu daga cikin masu tsaron lafiyar Shugaba Erdogan ya fito ne bayan wani hargitsi da ya auku a ranar 16 ga watan Mayu lokacin ziyarar da Erdogan ya kai babban birnin na Amirka, inda aka ji wa masu zanga-zanga tara rauni a wajen gidan jakadan Turkiyya.

Martin Schäffer shi ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen Jamus da ya ce dokokin Jamus za su yi aiki a kan jami'an tsaron matukar sun shigo kasar.

Ya ce: "Ba zan so in yi bayani dangane da abinda ya faru a Washington lokacin ziyarar shugaban Turkiyya ba. Amma ina tabbatar da cewa a dalilin wannan lamari wasu daga cikin tawagar shugaban Turkiyya musamman masu tsaron lafiyarsa, akwai sammacin da duniya ta bayar na kamasu."

Da ma dai a watannin baya-bayan nan huldar dangantaka tsakanin Jamus da Turkiyya ta yi tsami.