1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukatar hadin kai don makomar Afghanistan

Abdullahi Tanko Bala
August 30, 2021

Ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas ya bukaci Rasha da China su shiga cikin tattaunawa kan makomar Afghanistan wanda ya hada da shirin kwashe 'yan Afghanistan da ke fuskantar barazana daga Taliban.

https://p.dw.com/p/3zhRG
Deutschland | Außenminister Heiko Maas | Afghanistan Statement
Hoto: Annegret Hilse/REUTERS

Ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas yace akwai bukatar Rasha da China su shiga cikin tattaunawar da ake yi game da makomar Afghanistan ciki har da shirin kwashe yan Afghanistan din da ke fuskantar barazana daga yan Taliban.

Yace taron gaggawa da kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya zai gudanar a birnin New York nan gaba a wannan Litinin zai fayyace ko Moscow da Beijin suna da niyyar bada hadin kai ko kuma a'a.

Sabanin sauran wasu wakilai masu kujerar dundundun a kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniyar, kasashen Birtaniya da Faransa da Rasha da kuma China sun cigaba da barin ofisoshin su na jakadanci a bude a kasar ta Afghanistan da ke karkashin 'yan Taliban.

Jamus na shirin karbar mutane kimanin 40,000 wadanda suka hada da tsofaffin ma'aikata 'yan Afghanistan da suka yi aiki da sojojin Jamus ko ma'aikatan gwamnati da kuma wadanda ke bukatar kariya ta musamman kamar mata da masu rajin kare hakkin dan Adam da iyalansu.