Jamus ta baiyana bacin ranta game da tsare sojojin Burtaniya a Iran | Labarai | DW | 27.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus ta baiyana bacin ranta game da tsare sojojin Burtaniya a Iran

Kasar Jamus dake shugabancin karba karba na Kungiyar Taraiyar Turai a yanzu tayi kiran jakadan kasar Iran dake nan Jamus tana mai baiyana bacin ranta game da kame sojojin ruwa 15 na Burtaniya da kasarsa tayi.

Mai magana da yawun maaikatar harkokin wajen jamus tace mataimakin ministan harkokin waje yayi kira da gaggauta sakin jamian na Buratniya haka kuma alhakin kula da lafiya da tsaron wadannan jamian duka suna hannun Iran .

Iran dai tace sai ta kammala bincike da takeyi domin tabbatr da ko da gangan wadannan sojoji suka keta kann iyakokinta

A halinda ake ciki kuma firaministan Burtaniya Tony Blair yace zasu dauki mataki na gaba game da wannan batu tunda Iran tayi kunnen uwar shegu da kira da ake mata na sakin wannan sojoji kodayke bai baiyana ko wane mataki zasu dauka ba.