1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta bai wa Ukraine karin tallafi

Abdullahi Tanko Bala
August 11, 2022

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya sanar da gagarumin karin tallafin kudi da makamai ga kasar Ukraine a kokarin da ta ke yi na dakile mamayar da Rasha ta yi mata da ya faro watanni shida da suka gabata.

https://p.dw.com/p/4FQJw
Sommer-Pressekonferenz Bundeskanzler Olaf Scholz
Hoto: Political-Moments/IMAGO

Scholz yace yakin na bukatar daukar kwararan matakai na tallafa wa Ukraine a kokarin da ta ke yi na kare 'yancin kasarta.

"duk alhakin wannan yakin ya rataya a wuya shugaban Rasha. Shi ya haddasa wannan mummunan al'amari, yakin da ba za a lamunta da shi ba."

A waje guda kuma shugaban gwamnatin na Jamus Olaf Scholz ya bada shawarar gina bututun mai daga Portugal ya ratsa ta Spain da Faransa zuwa tsakiyar Turai domin kawar dogaron kasashen Turai akan makamashin Gas na Rasha.

Yace ya tattauna batun da shugabannin Spain da Faransa da kuma  hukumar tarayyar Turai a Brussel.