Jamus ta ba da tabbacin ci gaba da aikin da take yi a Afganistan | Labarai | DW | 21.06.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus ta ba da tabbacin ci gaba da aikin da take yi a Afganistan

A yayin ziyrarsa a yankin Mazar-i-Sharif na kasar Afganistan ministan tsaron Jamus, Thomas de Maiziere ya ce kasarsa za ta ci gaba da aikin da take yi a arewacin kasar in har an cika sharuddan yin hakan

A karshen ziyararsa ya kuma gana da gwamnan wannan lardi Mohamed Atta inda suka yi magana game da bukatar shiga tattaunawar samar da zaman lafiya tsakanin gwamnatin Afganstan da 'yan Taliban. Ita dai gwamnatin Amirka ta bayyana niyarta ta hawa teburin tattaunawa tare da Taliban domin yin musayar firsinoni. Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amirka, Jennifer Psaki tac e mai yiwuwa ne Taliban ita kuma ta nemi yin musayar firsinonin da ake tsare da su a sansanin gwale-gwalen Amirka da ke Guantanamo. Amirka ita kuma za ta so Taliban ta ba ta ba da tabbacin sakin sojanta, Bowe Beghali da take tsare da shi tun shekarar 2009 da kuma tabbacin komawarsa gida Amirka lamin lafiya.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Zainab Mohammed Abubakar