Jamus ta amince da bai wa baƙi fiye da dubu 20 da ke zaune a nan ƙasar takardun izinin zama. | Labarai | DW | 17.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus ta amince da bai wa baƙi fiye da dubu 20 da ke zaune a nan ƙasar takardun izinin zama.

A taron da suke yi a birnin Nürnberg, ministocin harkokin cikin gida na jihohi 16 na tarayyar Jamus, sun cim ma madafa a kan ce-ce ku cen da suke yi, na bai wa baƙi kusan dubu ɗari 2 da ke zaune a nan kasar takardun izinin zama. Su dai waɗannan baƙin, dukkansu sun taɓa neman mafaka a nan Jamus, amma aka yi watsi da bukatunsu, sai dai ba a kore su da ƙasar ba, suna nan zaune ne tamkar baƙin da aka haƙura da su, ba tare da ba su cikakkun izinin zama ba. Duk da wannan yarjejeniyar dai, wasu jihohin, musamman inda jam’iyyun CDU na ’yan mazan jiya ke mulki, na ɗari-ɗari da amincewa da shirin. Wani kakakin jam’iyyun CDU da CSU a kan batutuwan harkokin cikin gida Norbert Gneis, ya kare matsayin da suka ɗauka ne da cewa:-

„Idan muka fara bai wa baƙin takardun izinin zama, ba tare da mun tabbatar cewa suna da aikin yi ba, to za mu ƙiƙiro wata sabuwar matsala ke nan ga duk al’umman ƙasar nan baki ɗaya, ko muna so ko ba ma so. Zai iya yiwuwa, a karshen wa’adin shekaru biyun da za a ba su, su kasance har ila yau ba su da aikin yi, abin da zai sa a mai da su zuwa matsayinsu na da, wato na waɗanda ake haƙura da su. Aiwatad da wannan shirin kamar yadda mafi yawan ministocin harkokin cikin gidan jihohin suka amince da shi dai, zai kasance wani abu ne mai wuya."