1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Zargin 'yan majalisa da rashawa

Zainab Mohammed Abubakar
January 30, 2020

'Yan sandan Jamus ta kai somame a ofisoshi da gidajen wata 'yar majalisar jam'iyyar shugabar gwamnati Merkel ta CDU da wani tsohon dan majalisar CSU, kan zargin rashawa.

https://p.dw.com/p/3X4A4
Deutschland Ermittlungen im Fall Lübcke
Hoto: Reuters/R. Orlowski

Masu shigar da kara a birnin Frankfurt sun ce, wajen jami'an 'yan sanda 100 ne suka gudanar da wannan somame daban daban a kan 'yar majalisa Karin Strenz da tsohon dan majalisa Eduard Lintner na jam'iyyar tagwaitakar CDU watau CSU da ke Bavaria.

A yayin somamen, an gudanar da bincike a jihohin tarayya na Mecklenburg-Western Pomerania da Bavaria, da Berlin da kuma kasar Beljium bayan cirewa Strenz rigar kariya ta majalisa da safiyar yau Alhamis.

Ana zargin 'yan siyasar biyu da laifin karbar kudi da yawansu yakai euro dubu 22, domin neman alfarma wa gwamnatin Azerbaijan a majalisar Turai.