1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Shekaru 70 na kundin tsarin mulki

May 23, 2019

Batun fara aiki da kundin tsarin mulkin na Jamus ya wakana ba tare da sa-in-sa ba da masu ra'ayin gurguzu abin da babu wanda ya taba tunanin haka kafin wancan lokaci.

https://p.dw.com/p/3Ix2p
Deutschland Bonn Bundestag stimmt Einigungsvertrag zu
Hoto: picture-alliance/dpa/R. Holschneider

Kundin ya mayar da hankali kan karfafa al'umma maimakon ba da fifiko kan gine-gine na zamani, kundin ya fito karara cikin jimlolin farko kan kare hakkin jama'a. Ba da fifiko ga mutane ba abu ne da tsarin gurguzu ya damu da shi ba. Miliyoyin mutane kan sha wahala, ko gallazawa har da mutuwa. Yanzu wannan martaba ta zama abin mayar da hankali.

Tsarin mulkin da aka yi aiki da shi gabanin na yanzu, ya zama na zamani a wancan lokaci. Shi ma ya kunshi kare hakkin dan Adam da bai wa mata 'yancin zabe a Jamus. Amma kundin bai kare samun 'yan kama karya da gurguzu ba. Irin abin da aka gani karkashin wancan tsarin mulkin lokacin Jamhuriyar Weimar da ake aiki da shi gabanin zuwan dan kama-karya Adolf Hitler kan madafun gwamnatin Jamus. A ganin Farfesa Ulrich Battis masanin sharia tilas ko yaushe a samu wadanda za su kare tsarin mulki:

Deutschland Rechtsprofessor Ulrich Battis
Farfesa Ulrich Battis masanin doka a JamusHoto: picture-alliance/dpa

"Jamhuriyar da ta gabace ta ba ta gaza ba sakamakon rashin kundin tsarin mulki mai karfi, amma sai saboda rashin masu girmama dimukuradiyya da yawa."

Wancan tsarin ya zama mai sarkakiya da wuya saboda shugaban kasa na da karfin rushe majalisar dokoki karkashin dokar gaggawa, lamarin da ya taimaki Adolf Hitler. Amma yanzu shugaban kasa yana da karfi na wakilci ne kadai. Karkashin wannan kundin tsarin mulkin an karfafa karfin shugaban gwamnati da majalisar dokoki.

An duba matsalolin tsarin mulkin da aka yi amfani da shi gabanin wannan gami da matsalolin 'yan gurguzu domin shinfida sabon kundin tsarin mulki, ga lokaci na musamman Jamus tana dare gida biyu a shekarar 1949. Bayan sake hadewar Jamus a shekarar 1990 maimakon sabon kundin tsarin Jamus ta Gabas ta shida aikin da wannan tsarin mulkin na Jamus ta Yamma, kamar yadda jagororin siyasa na lokacin suka amince.

Har yanzu kundin tsarin mulkin yana da karbuwa tsakanin al'umma kuma a cewar Farfesa Ulrich Battis masanin dokoki akwai dalili:

Deutschland 70 Jahre Grundgesetz
Hoto: Imago Images/C. Ohde

"Kotun tsarin mulki tana da gagarumin karfi, kuma karfin ya samo asali daga kundin tsarin mulkin tarayya da ake aiki da shi. saboda kotun tsarin mulki ta tarayya ta fassara kundin tsarin mulki ta hanyar sassaucin ra'ayi da bayar da karfi ga mutane maimakon gwamnati. Tsarin mulkin ya samu karbuwa tsakanin mutane."

Har yanzu ana godiya ga mutanen da suka tsara wannan kundin mai tasiri ga Jamus.