Jamus: Schulz zai nemi shugaban gwamnati | Siyasa | DW | 25.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Jamus: Schulz zai nemi shugaban gwamnati

Jam'iyyar SPD a Jamus da ke cikin gwamnatin hadakar kasar, ta sanar da amince wa da tsohon shugaban majalisar Tarayyar Turai Martin Schulz a matsayin wanda zai tsaya takarar shugaban gwamnatin.

Watanni takwas gabanin zaben na Jamus ne dai mataimakin shugaban gwamnatin kana ministan tattalin arziki wanda kuma ya kasance shugaban jam'iyyar hadakar gwamnati ta SPD Sigma Gabriel ya bayyana Martin Schulz din a matsayin wanda zai fafata da shugabar gwamnatin kasar ta yanzu Angela Merkel da ta kasance 'yar jam'iyyar CDU, a zaben mai zuwa na Bundestag. Gabriel ya bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labrai da suka gudanar a ranar Talata 24 ga wannan wata na Janairu da muke ciki, inda ya ce:

"Martin Schulz shi ne dan takarar shugaban gwamnati daga jam'iyyar SPD a zaben Bundestag mai zuwa na 2017. Wannan shi ne abin da jam'iyyarmu ta amince da shi yayin taron da muka gudanar, kana shi ne zamu gabatar wa da shugabannin gudanarwar jam'iyyar a taron da za mu yi a ranar Lahadi 29 ga wannan wata na Janairu domin amince wa da shi. Martin Schulz shi ne kuma zai gajeni a matsayin sabon shugaban jam'iyyar SPD kamar yadda baki dayanmu muka amince bayan da na gabatar da shawara. Shugabancinsa zai samu nasara ne idan har baki dayan jam'iyya ta amince da shi, ba kamar yadda a baya aka samu matsala tsakanin shugaban jam'iyya da dan takarar shugaban gwamnati ba."

Dama dai tuni jam'iyyar ta SPD ta amince da ministan harkokin kasashen ketare na Jamus din Frank-Walter Steinmeier a matsayin wanda zai kasance shugaban kasa, kana Sigmar Gabriel ne zai gaji mukaminsa. Da yake nuna jin dadinsa kan wannan batu Gabriel cewa ya yi:

"Zan mika godiyata ga jam'iyyarmu bisa yanke shawarar in gaji mukamin ministan harkokin kasashen ketare daga Frank-Walter Steinmeier, haka kuma shugabannin jam'iyyarmu sun amince da tsohuwar sakatariyar gwamnati kana mataimakiyar ministan tattalin arziki Brigitte Zypries ta gaje ni a matsayin ministar tattalin arziki da makamashi. Zaben da za a gudanar a Jamus a nan gaba na Bundestag, zai sha ban-ban da sauran zabukan da aka gudanar. Ba wai kawai zai zama yanke hukunci ga yadda Jamus za ta kasance nan gaba bane harma da yadda za a samu kwanciyar hankali a Tarayyar Turai. Jamus ta zama wata ja gaba a fannin kwanciyar hankali, ya kamata ta tabbatar da ganin an samu kwanciyar hankalin a sauran kasashe."

A nasa jawabin tsohon shugaban majalisar Tarayyar Turan kana dan takarar shugaban gwamnatin Jamus a zaben na Bundestag karkashin jam'iyyar SPD Martin Schulz cewa ya yi:

"Akwai gagarumar matsala a cikin al'umma ba wai kawai a kasarmu ba har ma da sauran kasashen Turai. Al'ummar kasashen Turai na sake rarrabuwa, bayan zaben shugaban kasa a Amirka dole a yi tunanin cewa al'ummar dniya na rarrabuwa. Muna son mu yi yakin neman zabe da zai bai wa jam'iyyarmu ta Social Democrats damar yin shugabanci. Kasarmu na bukatar sabon shugabanci a wannan yanayi na rintsi."

An dai tambayi Sigma Gabriel dalilin da ya sanya bai tsya takarar ba amma ya bayar da sunan Martin Schulz inda ya amsa da cewa saboda Schulz ya fi shi dama. Ya ce a matsayinsa na shugaban jam'iyyarsu ta SPD ya kamata ya kasance yana da damar zabar wanda ya san zai iya, kuma hakan ce ta sanya ya bayar da sunan Martin Schulz saboda ya san zai iya. Za dai aga yadda za ta kaya a zaben na Bundestag nan da watanni takwas masu zuwa, musamman tsakanin jam'iyyaun SPD da CDU da abokiyar tagwaitakarta ta CSU, wadanda suka dade suna kawance a karkashin gwamnatin hadaka a Jamus.

 

Sauti da bidiyo akan labarin