Jamus: Scholz na neman shugabancin SPD | Labarai | DW | 16.08.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus: Scholz na neman shugabancin SPD

Ministan kudi na Jamus Olaf Scholz, zai gabatar da kansa a matsayin dan takarar shugabancin jam'iyyar SPD, karamar abokiya, a gwamnatin hadakar da Angela Merkel ke jagoranta.

Majiyar jam'iyyar a Berlin na nuni da cewar, tun a farkon wannan makon ne dai Scholz da ke zama mataimakin shugabar gwamnati, ya sanar da manufarsa, a yayin wata ganawa ta wayar tarho da shugabannin riko na jam'iyyar SPD Malu Dreyer da Manuela Schwesig da Thorsten Schaefer-Guembel.

Tuni dai Scholz ya fara neman abokin tafiya a wannan fafutukar tasa.