Jamus: Rasha ta jinjinawa yunkurin Jamus game da zaman lafiya a Libiya | Labarai | DW | 29.12.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus: Rasha ta jinjinawa yunkurin Jamus game da zaman lafiya a Libiya

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaba Vladimir Putin na kasar Rasha sun bukaci amfani da siyasa da kuma huldar jakadanci domin warware rikicin kasar Libiya.

Tun da farko an bayyana sanya bakin Jamus da Majalisar Dinkin Duniya a rikicin na Libiya, a matsayin hanya daya tilo da zata kawo karshen rikicin gwamnati da na dakarun janar Khalifa Haftar. A farkon wannan wata na Disamba ne shugaba Putin na Rasha ya yabawa kokarin Jamus na kirkirar matakan da za a bi don zaman lafiya ya samu a kasar. Kasar Libiya dai ta shiga yakin basasa ne bayan hambarar da gwamnatin shugaba Moamer Gaddafi a shekara ta 2011.