Jamus da Rasha na yunkurin hana farmakin Idlib
September 14, 2018Mista Maas ya ce, kowa na sane kan hadarin da dubban jama'a za su fada ciki, muddun aka kai wannan farmaki a kokarin kwace ikon birnin da gwamnatin shugaba Bashar al-Assad mai samun goyon bayan kasashen Rasha da Iran da Turkiya ke yunkurin yi.Ministocin biyu za su gana a yau a birnin Berlin.
Majalisar Dinkin Duniya da kasashe masu fada a ji, suna ci gaba da yin gargadin kaucewa aukuwar abin da suka kira, babban bala'i ga dubban fararen hula da ke yankin, sun ce kuskure ne mai girman gaske yin hakan, ganin rayukan da ka iya salwanta.
Gwmantin Siriya dai ta tura dubban sojoji yankin, inda za su yi anfani da karfi don fatatakar 'yan tawayen da aka yi kiyasin sun kai dubu talatin. Rasha na daga cikin kasashen da ke marawa gwamnatin Assad baya don ganin ta sami galaba a rikicin kasar na sama da shekaru bakwai.