Jamus na fuskantar barazanar ′Yan ta′adda | Siyasa | DW | 13.10.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Jamus na fuskantar barazanar 'Yan ta'adda

A sakamakon barazanar hare-hare daga 'yan ta'adda Jamus ta fara ɗaukar tsauraran matakai na tsaro

default

Hotunan barazanar kai hari a Jamus

Barazana iri daban-daban da aka samu ta yanar gizo na yin nuni da cewar Jamus zata fuskanci hare-haren ta'addanci daga masu zazzafar aƙidar Islama. A sakamakon haka aka ɗauki tsauraran matakan tsaro a filayen saukar jiragen sama da tashoshin jiragen ƙasa da hanyoyin dogo na ƙarkashin ƙasa. Su dai masu iƙirarin jihadin suna buƙatar ganin Jamus ta janye sojojinta ne daga Afghanistan.

Su dai masu barazanar kawo hare-haren ta'addancin nan Jamus suna amfani da shafuna ne na yanar gizo masu taken:"Zamanin Shahada" ko "Al-Faluja" a harsunan larabci ko turkanci ko rashanci tare da canje-canjen sunayen a cikin ƙiftawa da Bisimillah. Amma waɗanda ake gabatar da kiraye-kirayen gare su, waɗanda matasa ne musulmi da aka cusa musu zazzafan ra'ayin akida sun san yadda zasu kai ga ainifin shafin na yanar gizo dake ɗauke da fina-finan bidiyo na al'qa'ida da sauran ƙungiyoyi masu ra'ayin ta'addanci. Ta shafin na yanar gizo akan ba da sanarwar tarukan da aka shirya da wuraren da za a gudanar da su. Manufar fina-finan na biyo dai shi ne su yaɗu zuwa dukkan sassa na duniya a cikin ƙiftawa da Bisimillah tun kafin jami'an tsaron ƙasashen yammaci sun an kara su kuma toshe layukan. Kuma a haƙiƙa baya ɗaukar wani lokaci mai tsawo kafin fina-finan su yaɗu har ya zuwa shafin youtube, wanda shi ne shafin bidiyo ta yanar gizo mafi giram a duniya. Babban misali a nan shi ne wasu fina-finan biyo da wani mai zazzafan aƙida da ake kira Bekkay Harrach dake nan birnin Bonn ya gabatar kwanan baya. Da farko wasu 'yan ƙalilan dake da masaniya game da shafinsa suka gano fina-finan kuma nan take suka shigar da su cikin shafin youtube, kuma a halin yanzu haka zaka samu ɗaruruwansu a yanar gizo. A sakamakon wannan ci gaba ake ɗaukar tsauraran matakan tsaro a filayen saukar jiragen sama da tashoshin jiragen ƙasa da hanyoyin dogo na ƙarƙashin ƙasa a duk faɗin ƙasar ta Jamus. Wani bincike da DW ta gudanar a filin saukar jiragen sama na Köln/Bonn ta samo ra'ayo daban-daban na matafiya Jamusawa a game da wannan barazana. Ga dai wasu matafiyan da aka nemi jin ta bakinsu.

Bundespolizei / Flughafen Frankfurt / Terror

Matakan tsaro a filin jirgin sama

"Ba shakka na da tasiri zuciyata. Mutum na tunani daban-daban, amma a halin yanzu ana iya ganin jami'an tsaro sun barbazu ko'ina. Amma fa idan mutun na tsaron abkuwar wani abu sai kawai yayi zamansa a gida."

"A gaskiya ina tare da 'yar damuwa. Amma na yi imanin cewar jami'an tsaronmu zasu yi bakin ƙoƙarinsu wajen kadagarkin duk wani abin da zai faru."

"A'a sam ban damu ba. Mun fuskanci irin wannan barazanar dangane da bukukuwan oktoba a birnin Munich. Amma duk da haka an gudanar dasu salin-alin ba abin da ya faru."

A dai halin da ake ciki yanzun galibi masu zazzafar aƙidar sun fara ficewa daga Jamus don neman horo a sansanonin 'yan ta'adda a iyakoki tsakanin Afghanistan da Pakistan ko arewacin Afrika. Mahukuntan sun lura da dozin-dozin na irin waɗannan masu zazzafar aƙida da suka bar Jamus akan wannan manufa a cikin watanni goma sha biyu da suka wuce. Da yawa daga cikinsu, da mahkuntan ke da ra'ayin cewar suna iya zama barazana bayan sun dawo ko kuma ga sojojin Jamus dake Afghanistan.

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu