1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Steinmeier ya nuna rashin dacewar gangami

Zainab Mohammed Abubakar
August 30, 2020

Shugaba Frank-Walter Steinmeier da sauran manyan jami'an gwamnatin Jamus, sun yi Alla-wadan gangamin adawa da matakan yaki da corona da masu tsattsauran ra'ayin rikau suka yi.

https://p.dw.com/p/3hlmW
Deutschland Präsident Frank-Walter Steinmeier | Kampf mit Maske
Hoto: picture-alliance/AP Photo/K. Joensson

Steinmeier ya ce ko kadan, gwamnati ba zata lamunci yadda aka rika wasa da tutocin majalisar da na masu ra'ayin rikau din a gaban ginin majalisar ba, saboda yin hakan na zama kalubalantar tsarin demokradiyyar kasar kai tsaye.

Ya kara da cewar, doka ta amincewa duk wanda ke adawa da matakan yaki da COVID-19 da gwamnati ta tsara, na fitowa fili ya bayyana ra'ayinsa, koda kuwa a bainar jama'a ne, amma ba ta hanyar cin zarafin gwamnati saboda dalilai na siyasa ba.