Jamus: Kisan Walter Lübcke na daukar hankali | Labarai | DW | 26.06.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus: Kisan Walter Lübcke na daukar hankali

Ma’aikatar cikin gidan Jamus ta ce mutumin nan mai ra’ayin 'yan NAZI ya jaddada daukar alhakin nauyin bindige dan siyasar nan mai ra’ayin tallafa wa 'yan gudun hijira Walter Lübcke na jam’iyyar CDU a gidansa.

A yayin wani taro na musamman a asirce kan batun kisan dan siyasar da majalisar dokokin Jamus ta Bundestag ta gudanar, ministan cikin gidan Horst Seehofer ya ce wanda ya yi kisan ya tabbatar wa jami’an bincike da cewa shi kadai ne ya yi aika-aikar ba wai tura shi a ka yi ba, kana kuma a share daya ministan na cikin gidan na Jamus ya ce hukumomi za su ci gaba da binciken lamarin domin gano ko da akwai hannun wani a ciki, duk da yake wanda ya yi ta'addin ya nuna cewa ba ya tare da kowa.