Jamus: Kame 'yar IS a Frankfurt | Labarai | DW | 16.11.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus: Kame 'yar IS a Frankfurt

'Yan sanda a birnin Frankfurt na kasar Jamus sun kame wata 'yar IS jim kadan bayan saukarta daga jirgin da ya kawo ta daga Turkiyya wacce ta izo keyar matar Bajamusa zuwa gida.

BdT Lufthansa Streik

'Yan sanda a nan Jamus sun kama wata mata 'yar kungiyar IS a filin jirgin sama na birnin Frankfurt jim kadan bayan saukarta daga jirgin da ya kawo ta daga Turkiyya wacce tiso keyarta zuwa kasar ta Jamus.

 Hukumomin shari'a na kasar ta Jamus dai sun cabke matar mai suna Nasim A a bisa zargin kasancewa mamba a wata kungiyar 'yan ta'adda ta ketare. A shekara ta 2014 ne Nasim A ta koma da rayuwa a kasar Siriya inda daga bisani ta auri wani mayakin kungiyar IS, wanda ya ja ta suka koma Iraki da zama.

 Amma daga baya sun sake komowa a Siriya inda a can ne a farkon shekara ta 2019 mayakan Kurdawa suka kame su.