Jamus: Hari ya raunata mutum guda | Labarai | DW | 02.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus: Hari ya raunata mutum guda

'Yan sandan Jamus na neman wani mutum da ya kai harin bindiga a birnin Bremen da safiyar wannan Alhamis.

Mutum guda ya samu mummunan rauni, lokacin da wani dan bindiga ya buda wuta cikin wani babban shagon sayar da kayayyaki, a birnin Bremen da ke yankin arewacin Jamus.

Rahotanni na nuni da cewar, yanzu haka jami'an tsaro sun duka ka'in da na'in wajen neman mutumin da ake zargi da kai harin, wanda aka bayyana da ka iya kasancewa babban hadari ga jama'a.

Sai dai har yanzu babu wani bayani daga bangaren 'yan sanda dangane da harin na birnin Bremen.