1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Hana sanya Burka ya kusa zama doka

Yusuf Bala Nayaya
April 28, 2017

'Yan majalisa a Jamus sun amince da kwaryakwaryar doka da ta tanadi haramta sanya hijabin nan samfurin Burka da mata Musulmi ke sanyawa.

https://p.dw.com/p/2c2id
Eine verschleierte Frau im Niqab neben einer Polizistin
Hoto: picture-alliance/dpa/F.Schuh

Wannan dai na zuwa ne bayan lokaci da aka dauka ana kai hare-hare nan da can a kasar, ciki kuwa har da harin da aka kai kasuwar Kirsimeti a birnin Berlin da ya yi sanadi na rayukan mutane 12. Har-ila-yau matakin na zuwa gabannin babban zabe da kasar za a yi a watan Satumba.

Wannan doka dai ta bambamta da ta Faransa wacce ta haramta sanya nau'in hijabin a dukkanin wajen taron jama'a. Ta dai haramta sanya Burkan ne ga jami'ai na gwamnati lokacin aikinsu kamar jami'an zabe da sojoji da ma'aikatan shari'a.

Miliyoyin al'umma ne dai suka shiga kasar ta Jamus don neman mafaka mafi akasari daga kasashe masu rinjaye na Musulmi. Akwai bukatar majalisar dattawa ta (Bundesrat) ta amince daftarin dokar kafin ya zama doka a Jamus.