Jamus: Hadin kai domin yaki da Corona | Labarai | DW | 03.04.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus: Hadin kai domin yaki da Corona

Ministan kiwon lafiya na Jamus Jens Spahn ya ce 'yan kasar sama da miliyan hudu da dubu dari uku suka karbi zagayen farko ko kuma suka kammala karbar rigafin Corona.

Shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier a sakonsa na zagayowar bukukuwan Ista na wannan shekarar, ya bukaci al'ummar kasar da su mara wa gwamnati baya yayin da take yaki da annobar coronavirus ko COVID-19 zagaye na uku duk kuwa da kuskuren da yace mahukuntan sun yi a baya.

Hakan ba zai rasa nasaba da zanga-zangar da aka gudanar a Stuttgart, ta adawa da matakan yaki da annobar. Haka kuma kungiyar likitoci ta kasar tace ba za ta lamunci nuna wariya wajen bayar da allurar a tsakannin yan kasar ba.