1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta cimma matsaya kan bakin haure

Abdul-raheem Hassan
July 6, 2018

Hadakar jam'iyyun kawance ta CDU/CSU da SPD da ke mulki a Jamus, sun dai-daita kan batun 'yan gudun hijira da tsarin neman mafaka mai cike da sarkakiya don ceto gwamnati.

https://p.dw.com/p/30v8y
Deutschland Bundestag 45. Sitzung | Aussprache Kanzleretat | Seehofer & Scholz & Merkel
Hoto: picture-alliance/Anadolu Agency/A. Hosbas

Bayan ganawar kwanaki biyu a birnin Berlin, sabuwar shugabar jam'iyar SPD ta 'yan gurguzu Andrea Nahles ta ce jam'iyyun sun cimma matsaya kan sake fasalin neman mafakar siyasa a Jamus a wani mataki na cimma kyakyawar mafita kan matsalar da ke neman raba kawancen jam'iyyun da ke shugabanci.

A baya dai jam'iyyar SPD ta cije kan kin amincewa da matakan da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta gabatar kan batun 'yan gudun hijira, sai dai Merkel ta jaddada bukatar tsaurara bincike kan iyakar kasar tare da samar da sansanonin taka wa 'yan gudun hijira birki a tsakanin Jamaus da Austiriya.