Jamus da Turkiyya an sasanta | Labarai | DW | 17.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus da Turkiyya an sasanta

Gwamnatocin Jamus da Turkiyya sun amince da bayar da himma ga harkokin bunkasa kasashen biyu bayan takaddamar da ta wakana tsakaninsu mai nasaba da tsare wani dan jarida a Turkiyya a bara.

54. Münchner Sicherheitskonferenz MSC - Sigmar Gabriel und Mevlüt Cavusoglu (picture alliance/dpa/S. Hoppe)

Sigmar Gabriel tare da Mevlut Cavsoglu na Turkiyya

Ministocin harkokin wajen kasashen Jamus da Turkiyya, sun bayyana aniyar kyautata hulda tsakanin kasashen biyu ta fannonin tsaro da kuma tattalin arziki, bayan sakin dan jaridan nan Bajamushe mai asali da Turkiyya Denis Yücel a jiya Juma'a. A cewar Mevlut Cavusoglu wanda shi ne ministan harkokin wajen Turkiyya, manyan kasashen biyu, sun shawo kan daya daga cikin takaddamar da ke tsakaninsu, don haka ba tare da wata-wata ba, kamata ya yi su koma ga harkokin da za su kai su gaba.

Shi ma a nashi bangaren ministan harkokin wajen Jamus Sigma Gabriel, cewa ya yi ba laifi bane a sami sabanin ra'ayi tsakanin Jamus da Turkiyya, sai dai kuma lallai ne a martaba juna saboda makomar kasashen biyu. Zaman jarum na shekara guda dan jarida Deniz Yücel ya yi a Turkiyyar bisa zargin ta'addanci dai ya tsananta huldar diflomasiyya tsakanin Jamus din da kuma makwabciyarta wato Turkiyyar.