1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus da Najeriya sun kulla yarjejeniyar kasuwanci

August 31, 2018

A kokarin kara dankon zumunci Jamus da Najeriya sun rattaba hannu kan wasu jerin yarjejeniyoyi biyu da suka shafi kasuwanci da kuma batun ‘yan gudun hijira.

https://p.dw.com/p/3473i
Nigeria Besuch der Kanzlerin Merkel
Shugabar Jamus Angela Merkel da shugaba Buhari na NajeriyaHoto: picture-alliance/AP Photo/A. Akunleyan

A ci gaba da kokarin kara danko na zumunci da kuma kasuwanci, shugabar kasar Jamus Angela Merkel ta kammala ziyarar Najeriya tare da rattaba hannu kan wasu jerin yarjejeniyoyi biyu da suka shafi kasuwanci da kuma batun ‘yan gudun hijira.

Duk da cewar ana kallon ziyarar a matsayin wani kokari na kara habbaka kasuwanci da tattalin arziki, ziyarar ta Merkel ta tabo  muhimman batutuwa kan ‘yan gudun hijira da kuma kokarin taimakon matasa da sana’oi.

Ana dai kallon ziyarar a matsayin ci gaba a kokarin samun sabbin abokan huldar kasuwanci bisa la’akari da kokarin Birtaniya na  ficewa daga kungiyar Tarrayar Turai dama raba gari a tsakanin Turan da Amurka.

Nigeria Reise Bundeskanzlerin Angela Merkel
Shugabar Jamus Angela Merkel tare da shugaba Buhari na NajeriyaHoto: DW/U. Musa

Yawan al’ummar Najeriyar sama da milyan 200 dama dubun dubata na damammaki na kasuwanci ne ya dauki hankalin Jamus a fadar Merkel wadda ta ce tana shirin habbaka cinikayya  a tsakanin kasashen biyu.

Jamus din da Najeriya sun kulla yarjejeniyoyi guda biyu da suka hada da samar da dama ta basuka don harkokin noma da kuma sake farfado da kamfanin mota kirar Volkswagen da ta yi dogon suma baya.

Mittelmeer Migranten und Flüchtlinge in Schlauchboot
Wasu 'yan gudun hijira cikin kwale kwale a tekun Bahar MaliyaHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Diab

Batun ‘yan gudun hijirar ma dai ya dauki hankalin shugabannin biyu in da Jamus ta ce tana shirin aiki tare da tarrayar Najeriya da nufin dawo da ‘yan gudun hijirar kasar sama da dubu 30 da basu da izimin dama a can a kasar jamus din zuwa gida.

Shugabar ta Jamus ta kuma sanar da Karin damar karatu ga ‘yan Najeriya sama da 1200 a shekara.

A jawabinsa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce Najeriyar ba ta goyon baya tsallaka teku da nufin cin rani a ko’ina.

Shugabar gwamnatin Jamus ta gana kuma da shugaban hukumar zaben Najeriya Farfesa Mahmud Yakubu da nufin jin shirin zabbukan kasar da ke tafe. Zabbukan kuma da Shugaba Buhari ya yi alkawarin za su zamo mafi tsafta.