Jamus da Faransa na tattaunawa | Labarai | DW | 20.08.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus da Faransa na tattaunawa

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta isa gidan shakatawa na musamman na shugaban Faransa da ake kira Bregancon.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da mai dakinsa Brigitte ne suka tarbi Merkel din a wannan wurin shakatawa na musamman da aka gina shi a kan ruwan teku. 

Ana sa rai shugabannin za su tattauna kan siyasar duniya. Tuni ma dai Shugaba Macron ya sanar da cewa za su sanya ido sosai kan lafiyar jagoran adawar Rasha wanda ake zargin an sanya masa guba a abinci a safiyar Alhamis din nan. Ya kuma ce yana kira da ayi gaggawar dawo da mulkin farar hula a Mali.