Jamus da Faransa na jimamin tunawa da yakin duniya na farko | Labarai | DW | 29.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus da Faransa na jimamin tunawa da yakin duniya na farko

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da Francois Hollande na Faransa sun halarci bikin tunawa da dakarun kasashen biyu a yankin Verdun da ke a gabashin Faransa wadan da suka hallaka sakamakon yakin Duniya na farko.

Bikin jimamin wanda ya samu halartar 'yan Faransa da Jamusawa masu tarin yawa a wajen farfajiyar katafaren guri da ke nuna alamun irin yadda Faransawa da Jamusawa sama da dubu dari suka hallaka.

A yayin jimamin dai Shugaba Angela Merkel ta ce garin Verdun na daya daga cikin yake-yake mafiya muni da Duniya ta taba fuskanta.

Shugabar gwamnatin Jamus din ta kara da cewar:

"Shekaru dari da suka gabata dakarun Faransa dana Jamus sun yi gumurzun fada a nan,to amma duk da haka irin yadda aka karrama ni da nuna min faran- faran a matsayina na shugabar gwamnatin Jamus abin abin na dama ne."

Shima a nasa bangaren shugaban Faransa Francois Hollande ya ce a nan Verdun ne Francois Mitterand da shi da Helmut Kohl suka sha hannu domin karfafa dangantaka a tsakanin su.

Kimanin shekaru dari da suka gabata ne dai dakarun kasashen biyu suka fafata a garin Verdun wanda ya janyo asarar rayuka masu dumbin yawa daga dukkanin bangarorin biyu.