Jamus da Ecuador sun fara gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da nasara | Labarai | DW | 10.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus da Ecuador sun fara gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da nasara

Kungiyar kwallaon kafar Jamus ta fara gasar cin kofin kwallon kafa na duniya na karo 18 tare da yin nasara. A karawar farko ta bude gasar da suka yi jiya a birnin Munich ´yan wasan na Jamus dake samun horo daga mai koyar da ´yan wasa Jürgen Klinsmann sun lashe Costa Rica da ci 4 da 2. A karawa ta biyu da aka yi a filin wasa na Gelsenkirchen, Poland ta sha kashi a hannun Ecuador da ci biyu da nema. Shugaban tarayyar Jamus Horst Köhler ya kadamar da wasannin bayan wani kasaitaccen buki da aka yi filin wasa na Munich. Shugaban yayi tuni ga taken gasar ta bana wato Jamus na maraba da duniya baki daya sannan kuma ya yi fatan cewa wasan kwallon kafa zai hada kawunan al´umomin duniya. A nan Jamus dubun dubatan masu sha´awar wasan kwallo kafa suka kalli wasan ta manyan allunan da aka kakkafa a wuraren taruwar jama´a a fadin kasar. ´Yan sanda sun yaba da yadda ´yan kallo suka nuna halin ya kamata ba tare da an samu wani tashin hankali na a zo a gani ba.