Jamus: Bude taron ceto kamfanin Volkswagen | Labarai | DW | 02.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus: Bude taron ceto kamfanin Volkswagen

A kasar Jamus a wannan Laraba ce ake bude a birnin Berlin taron koli na duba makomar sana'ar kera motoci masu injin diesel da farfado da martabar kamfanin Volkswagen shekaru biyu bayan bankado badakalar injinan jabu.

A kasar Jamus a wannan Laraba ce ake bude a birnin Berlin taron koli na duba makomar sana'ar kera motoci masu injin diesel shekaru biyu  biyo bayan bankado badakalar injinan jabu da kamfanin Volkswagen ya yi a saman motoci kimanin miliyan 13 da ya sayar a kasashen duniya, matsalar da kuma ta ke yin barazana ga sana'ar sayar da motoci a duniya baki daya. 

Taron wanda zai hada wakillan gwamnati da na kamfanonin kera motoci na kasar ta Jamus zai tattauna matakan da ya kamata a dauka domin farfado da martabar sana'ar kera motoci wacce ke zama a matsayin ta biyar daga cikin fannonin da ke samarwa da kasar kudaden shiga tare da samar da guraben aiki dubu 800.

 A shekara ta 2015 ce dai hukumar kula da kare muhalli ta kasar Amirka ta bankado ha'incin da kamfanin na Volkswagen ya yi na dora wa injinan motocinsa na Diesel wata na'ura da ke boye gaskiyar yawan gurbatacciyar iskar gaz da suke fitarwa wanda ya saba wa doka a daidai lokacin da duniya ta dukufa ga yaki da dumamar yanayi.