Jamus: Bincike a masallatan Turkawa | Labarai | DW | 22.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus: Bincike a masallatan Turkawa

Ministan harakokin waje da takwaransa na ma'aikatar shari'a na Jamus sun yi kira zuwa ga tsaurara bincike da kuma sa ido a masallatan Turkawa da ke yin farfagandar shugaba Recep Tayyip Erdogan a Jamus. 

A ci gaba da takun sakar diflomasiyyar da ke wakana tsakanin Jamus da Turkiya, ministan harakokin waje da ma na ma'aikatar shari'a na kasar ta Jamus sun yi kira zuwa ga tsaurara bincike da kuma sa ido a masallatan Turkawa na nan Jamus da ke yin farfagandar shugaba Recep Tayyip Erdogan. 

Ministocin biyu sun bayyana a kungiyoyin da ke farfagandar goyon bayan Shugaba Erdogan a kasar Jamus da kasancewa wani babban hadari ga kasar.  Sun kuma bayyana bukatar ganin Jamus ta bayar da kariya ga 'yan Turkiya mazauna Jamus da ke kalubalantar farfagandar da Shugaba Erdogan ke yi a kasar ta Jamus. 

Kiraye-kirayen ministocin kasar ta Jamus na a matsayin martani ga kiran da Shugaba Erdogan ya yi zuwa ga 'yan kasarsa mazauna Jamus da kar su kada wa jam'iyyun SPD da CDU ta Angela Merkel kuri'arsu a zaben 'yan majalisar dokoki na 24 ga watan Satumba, ya na mai bayyana jam'iyyun a matsayin abokan gabar Turkiya.