Jamus: An kama wani da sayar da makamai ga dan bindiga | Labarai | DW | 16.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus: An kama wani da sayar da makamai ga dan bindiga

Jami'ai a Jamus sun ce sun kama wani mutum da ake zargi ya sayar da makamai da alburusan da wani dan bindiga da ke fama da cutar damuwa

Masu gabatar da kara sun ce mutumin Bajamushe ne mai shekaru 31 an kamashi ne a yammacin birnin Marburg. Dan bindigar wanda ya bude wuta da wata karamar bindiga samfurin Glock 17 a ranar 22 ga watan Yuli inda ya kashe mutane tara ya kuma jikkata wasu da dama kafin daga bisani ya kashe kansa. An yi imanin ya sayi bindigar ce a wata kasuwar bayan fage ta Internet da bata garin mutane