An gano wani tsohon littafi mai dauke da rayuwar Annabi Isa
July 31, 2024Wannan dadden littafin tarihi na Masar da ya shafe shekaru sama da 1,600 na dauke ne da labari kan rayuwar kuruciya ta Annabi Isa. Masana daddadun rubutun tarihi da suka gano wannan ittafin a wani dakin karatu da ke nan Jamus sun diga ayar tambaya kan bayanan da ke ciki inda suka ce yana da rauni. Lajos Berkes na daga cikin masanan da suka gano wannan littafin kuruciyar Yesu Almasihu, ya bayyanawa DW cewa hakan ba zai sauya duk wani abu da suka sani game da rayuwar Isa dan Maryam ba.
Ya ce "Wannan ba sabon tarihi ba ne na Yesu kuma ba shi da inganci, don haka ba zai sauya komai daga cikin abun da muka sani ba na koyarwar addinin Kirista saboda an samu rashin fahimta sosai a kan hakan kuma ba mu taba hakikancewa kan wani abu ba"
Duk da rashin yarda da ingancin bayanan, littafin na ci gaba da zama abun sha'awa a gare su saboda yana daga cikin rubutun farko na busharar Thomas wanda mujami'u suka yi watsi da shi kuma suka ki sakawa a cikin littafin sabon alkawari. Wanann littafin ya bayar da wani labari kuruciyar Yesu Almasihu, inda yake da shekaru 5 da haihuwa a lokacin da tsuntsun da ya gina da laka ya zama na zahiri.
Duk da cewa hakan ba ya kunshe a cikin tsohon alkawari, sai dai Busharar Thomas sananniya ce a wurin masana. Duk da cewa labaran da ke cikin wannnan littafi na zama abun mamaki ga wandanda suka san tarihin hakikannin rayuwar Annabi Isa musamman game da halayensa a lokacin da yake tasowa.
Wannan sabon littafi dai da masanan suka gano wanda ke dauke da kwanan wata na karni na 4 zuwa na 5 na nazari yanzu a kan kalmomi da rubuce-rubuce da ke sauyawa cikin karni. Lajos Berkes and Gabriel Nocchi Macedo na shirin sake fasalinsa da yin aikin fasara shi daga yaren Girka, kuma ana ganin hakan zai bayar da sabuwar fahimta kan harsunan da aka yi amfani da su.
Berkes ya kara da cewa " Hakan zai ba mu sabuwar fahimta kan harshen rubutun, inda zai fayyace salo da kuma ingancin rubutun da aka yi da harshen Girka ya fi yadda ake zato."
A yanzu haka dai a jami'ar Hamburg da ke nan Jamus akwai irie-iren wadannan litattafan fiye da 1000 inda yanzu haka uku bisa dari an sanya su a na'urar zamani, inda a nan ne masanan suka gano wannan tsohon littafin.
Ya ce " Alal hakika, wannan aikin a gefe yake sai dai kuma sai ya kasance babban abu gare mu, muna son mu kara zurfafa bincike bani da tabbaci sai dai kuma ina da yakinin cewa akwai makamantan wadannan littafan ko ma irinsa. Sai dai kawai ba sauki bane nemansu. Dole sai ka bi rukuninsu inda wani zai iya ganowa. Amma idan na ci sa'a zan iya gano wasu idan na jajjirci kuma na auna sa'a."
Har yanzu dai, yunkurin gano komai dangane da tarihin rayuwar Yesu da ya zarta wanda ke kunshe a cikin tsohon alkawari na ci gaba daukar hankali.