1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: An fasa gidan ajiye kayan tarihi a Dresden

Binta Aliyu Zurmi
November 25, 2019

Barayi sun fasa wani gidan ajiye kayan tarihi a birnin Dresden na Jamus, guda daga wurare masu muhimmanci da ake adana kayan tarihi masu daraja a nahiyar Turai.

https://p.dw.com/p/3TgGb
Deutschland Grünes Gewölbe Dresden
Hoto: picture-alliance/dpa/S. Kahnert

A wata sanarwar da jami'an 'yan sanda suka fitar, sun ce gidan adana kayan tarihin na Green Vault da ke fadar masarautar birnin na Dresden na da akalla kyayyakin masu daraja da suka hada zinare da  gwal sama da dubu hudu, wanda bisa kiyasi darajarsu ta kai ta sama da biliyan guda na euro.

Gidan aje kayan tarihi na Green Vault dai na daya daga cikin tsofafin gidajen da ke nahiyar Turai da August de Strong ya samar a shekarar 1723, kuma yana daya daga cikin gidaje tarihi goma sha biyu da birnin ke ji da su.

Wanna dai ita ce sata babba ta biyu da aka yi a Jamus a tsukin shekarun nan kuMA kawo yanzu ba a kai ga kama barayin ba.