Jamu na asarar Yuro Miliyan 50 akowace rana | Labarai | DW | 16.11.2007
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamu na asarar Yuro Miliyan 50 akowace rana

Yajin aikin matuƙan jiragen ƙasa a Jamus, ya haifar da tsaiko ga zirga-zirgar fasinjoji a ƙasar.Yajin aikin da a yau ya shiga rana ta uku, ya haifarwa miliyoyin Fasinjoji a ƙasar shiga cikin wani hali na damuwa.Rahotanni dai sun nunar da cewa akowace rana ta yajin aikin, Jamus na asarar Yuro miliyan 50. Ana dai sa ran kawo karshen wannan yajin aikinne, a safiyar gobe Asabar idan Allah ya kaimu. A yanzu haka tattaunawa game da shawo kan wannan rikici na nan na ci gaba da gudana.

 • Kwanan wata 16.11.2007
 • Mawallafi Ibrahim Sani
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/CI6m
 • Kwanan wata 16.11.2007
 • Mawallafi Ibrahim Sani
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/CI6m