Jammeh ya zargi ECOWAS da takalar yaki | Labarai | DW | 01.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jammeh ya zargi ECOWAS da takalar yaki

A sakonsa na sabuwar shekara, shugaban Gambiya Yahya Jammeh ya ce matsayar da kungiyar ECOWAS ta cimma ya sabawa dokarta na kaucewa tsoma baki a harkokin cikin gidan wata kasa.

Shugaba Yahya Jammeh ya zargi ECOWAS da aiyana yaki a kasarsa bayan da ta nemi ya sauka daga mulkin kasar sakamakon shan kayi da ya yi a zaben kasar. Kungiyar dai ta ECOWAS da ke da wakilci daga kasashe 15 na Yammacin Afirka ta bayyana cewa sakamakon zabe da aka yi a ranar daya ga watan Disambar bara ya halasta.

Shugaba Jammeh dai a sakonsa na sabuwar shekara a daren ranar Asabar ya ce matsayar da Kungiyar ECOWAS ta cimma ya saba wa dokarta na kaucewa tsoma baki a harkokin cikin gidan wata kasa. A cewarsa abin da kungiyar ta bayyana tamkar aiyana yaki ne a kasarsa da ma yi wa kasar kutse a kundin tsarin mulkinta, kuma abu ne da ba zai lamunta ba. Shugaban ya ce kasar ba za ta daga kafa ga kowa ba, kuma a shirye ta ke ta yaki duk wanda ya takaleta.

Zaben kasar ta Gambiya dai na watan Disambar bara ya bayyana madugun 'yan adawar kasar Adama Barrow a matsayin wanda ya lashe shi, sakamakon tda Shugaba Jammeh da ya shafe shekaru 22 a karagar mulki ya amince da shi  kafin daga bisani ya sauya matsayi.