Jam′iyyun kawance a Kwango sun gargadi shugaba Kabila | Labarai | DW | 14.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jam'iyyun kawance a Kwango sun gargadi shugaba Kabila

Gamayyar jam'iyyun Jamhuriyar Dimokradiyyar Kwango sun gargdi shugaban kasar da kada yayi watsi da kundin tsarin mulkin kasar.

A ranar Litinin din nan ce gamayyar jam'iyyun Jamhuriyar Dimokradiyar Kwango suka fada wa shugaban kasar Joseph Kabila cewar take-taken na hannun damansa na nuni da cewar yana kan haramar take tanade- tanaden kundin tsarin mulkin kasar.

Ta cikin wata takarda da ke kunshe da bayanan gargadin da aka rarraba wa manema labarai a kasar ta yi nuni da cewar shugaban gamayyar jam'iyyun da ake kira G7 na bukatar matakan gaggawa na tabbatar da ganin an gudanar da zaben shugabancin kasar da aka tsara a watan Nuwamba na shekara ta 2016.

Sanarwar ta kara da cewar keta kai'dojin kundin tsarin mulkin hatsari ne ga siyasar dimokradiyyar kasar da ta fuskanci yake- yake a shekarun 1996 da 2003 a inda daruruwan rayuka suka salwanta.

Kawo yanzu dai babu wani martani da ya futo daga fadar shugaban kasar kan kalaman na gamayyar jam'iyyun kasar.