1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam´iyyar URP ta lashe zaɓen da aka gudanar a Rasha

Ibrahim SaniDecember 3, 2007
https://p.dw.com/p/CVvj

Rahotanni daga Rasha sun nunar da cewa Jam´iyyar URP ta shugaba Vladimir Putin ce ke a kan gaba da yawan kuri´u, a zaɓen ´Yan majalisun dokoki. Jam´iyyar ta URP a zaben na jiya lahadi na da kashi 63 da digo uku, yayin da Jam´iyyar ´ Yan kwaminis ta tsira da kashi 11 da digo bakwai a cikin ɗari. Tuni dai Jam´iyyun adawa su ka yi watsi da sakamakon zaɓen da cewa an tafka magudi a cikinsa. Jam´iyyu 11 ne su ka fafata a wannan zabe, don neman kujerun Majalisar dokoki na ƙasar 450. Nasarar Jam´iyyar ta URP a cewar rahotanni, abune da ka iya bawa shugaba Putin damar ci gaba da taka rawa a fagen siyasar ƙasar, bayan ƙarewar wa´adin mulkinsa a watan Maris na shekara mai kamawa.