Jam′iyyar SPD ta lashe zabe a Berlin | Labarai | DW | 19.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jam'iyyar SPD ta lashe zabe a Berlin

Jami'iyyar CDU ta shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta kuma sha kaye a zabubbukan 'yan majalisu da ya gudana a birnin Berlin .

A yanzu dai ta tabbata cewa Jam'iyyar SPD ce za ta kasasnce jam'iyya mafi karfi da ikon fada a aji a majalisar jihar, biyo bayan lashe zaben 'yan majalisun jihohi da jam'iyyar ta yi a zaben da ya gudana a karshen mako inda jam'iyyar ta SPD ta samu kashi 21.6 a zaben, yayin da Jam'iyar CDU ta shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ke da kashi 18 cikin dari na kuri'un da aka kada, kana jami'yyar AFD ta masu kyamar baki a kasar da kashi 14.2 cikin dari.

Sakamakon zabubukan da ya nuna jam'iyyar CDU a matsayin ta biyu, na bayyana cewar jam'iyyar za ta rasa mulki a kawancen babban birnin kasar Jamus. To sai dai masu nazarin al'amuran siyasa dai na danganta rashin nasara da jam'iyyar CDU ta shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ke fuskanta a zabubbun kasar, baya rasa nasaba da yadda ta rungumi manufofinta a kan 'yan gudun hijira.