1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyyar FPI mai adawa ta kauracewa zaben kananan hukumomi

April 19, 2013

A daidai lokacin da ake gudanar da zaben kananan hukumomi har yanzu al'ummar Côte d' Ivoire na tunawa da irin rigingimmun da aka yi fama da su a zabubbukan baya wanda su ka haddasa asara duban rayuka.

https://p.dw.com/p/18JMY
Ivory Coast President Alassane Ouattara poses on the TV set of French channel TF1 prior to an interview that was part of the evening news broadcast, Tuesday Sept. 13, 2011 in Paris. (AP Photo/Fred Dufour, Pool)
Alassane OuattaraHoto: AP

Sama da mutane dubu ukku ne suka rasa rayukansu kana wasu dubbai suka fice daga gidajensu zuwa gudun hijira lokutan zabubukan shekarun 2010 zuwa 2011 a sakamakon riginginmun siyasar da suka biyo baya,wadanda suka raba kasar gida biyu bangaran kudu wanda ke karkashin ikon tsohon hambaran shugaba Laurent Gbagbo da kuma na arewaci, inda 'yan tawaye masu goyon bayan Alassane Outtara suka ja daga.

Wannan tashin hakali dai da aka yi fama da shi na zaman irin sa na farko da kasar wacce ta fi kowacce kwanciyar hankali a da a nahiyar Afirka ta fuskanta.

Mutane sun yi asara mummuna ta dukiyoyi da kadarori da kuma ta rayuka bila adadi , sai dai har yanzu duk da irin yunkurin da kungiyoyin kare hakki jama'a su ke yi irin su Amnesty Intenational na ganin an hukunta duk wadanda ke da hannu a cikin yamutsin, hakan ya kasa samuwa sai dai kawai na kusa da tsohon shugaba wato Laurent Gbagbo wanda kotun duniya ke tsare da shi ake kamasu ana hukuntawa wanda kuma wasu suke ganin babu adalci a cikin lamarin na shari'ar da suka ce ana nuna bambanci abinda wani dan kasuwa Daniel Djedje ya ce zancen ba haka yake ba rashin hakuri ne kwai na jama'a:

An Ivorian woman casts her ballot in presidential elections in Abidjan, Ivory Coast, 31 October 2010. Voters turned out in their numbers to cast their ballots in the historic elections, the first time in 10 years following years of delays and political intsability. EPA/NIC BOTHMA
Hoto: picture-alliance/dpa

"Ya ce a cikin sahun masu kayan sarki kama daga soja da jandarma da 'yan sanda duk wanda aka samu da laifukan an kulle su,aka kuma yi musu shari'a, kamata ta yi mutane su saka ido tare da yin hakuri su gani za a samu ci gaban abubuwa,ko da shi ke za a iya cewar al'ammura sun daidaita, to amma har yanzu shirin sake sasanta tsakanin al'umma na kasar da shugaba Alassane Ouattara ya kaddamar tun a cikin watan Janairu da ya wuce ya kasa samun nasara dangane da rarrabuwar kawunan da ake ci gaba da samu tsakanin 'yan kasar.

Ameli Kadjane wani dan kungiyar dake yin fafutuka ne, ya kuma ce shirin ba zai taba yin tasiri ba, inda bangarorin biyu su ka ci gaba da yiwa junansu kallon hadarin kaji:

Ya ce "ba zai yiwu ba a yi maganar sake sasantawa a siyasance ba tare da fada ma juna gaskiya ba, ba za a yi maganar shirin inda wadanda suka yi mulki a waccan lokaci basu fito ba suka nemi gafara ga jama'a dangane da abinda su kayi,ya ce kuma bai kamata ba wanda ke kan karagar mulki a yanzu su maimata irin kura-kuran da wadanda suka gabace su su kayi na yin shari'a maras adalci".

Da alama dai abubuwa na daf da yiwa Alassane Ouattara yawa ga rikicin siyasar sanan a daya hannu ga kungiyoyin ma'aikatsa na yin yaje-yajen aiki akan sha'anin kiwon lafiya da na samar da ilimi.Bugu da kari ga wani kudirin dokar da gwamnatin ta dauka, dake baiwa Alassane Outtara damar daukar wasu dokokin ba tare da tuntubar 'yan majalisun dokoki ba, kana kuma matsalar tsadar rayuwa.

Fatoumata Fofana wata ma'aikaciyar Banki ce a birnin Abidjan.

Voters wait in lines to vote at polling stations in Groupe Scolaire Saint Jeanne in the Abobo neighborhood of Abidjan, Ivory Coast, Sunday, Nov. 28, 2010. Ivorians went to the polls Sunday in a long-overdue presidential election that many hope will reunite the country eight years after a civil war divided it in two. Voters are choosing between president Laurent Gbagbo and the man he accuses of being behind the rebellion that sought to topple him, Alassane Ouattara. (AP Photo/Rebecca Blackwell)
Hoto: AP

Ta ce "dan abin cefane na uwargida bai wuce 'yar guntuwar leda ba, da mun sa ran samun sauyi sosai a kan wannan sabuwar gwamnati, amma a karshe mun yi la'asar da lamarinsu.Komai ya yi tsada mutane sun fara yanke kauna ga wannan gwamnati."

Kasar wacce ke da arzikin koko na daya daga cikin kasahen Afirka wadanda tattalin arzikin su ke ya kama hanyar daidaituwa,sai dai kuma jama'a na fama da talauci, kuma wannan zabe shine mataki na karshe na daddale tafarkin dimokaradiyya a kasar,to amma jam'iyyar adawa ta Laurent Gbagbo wato FPI ba ta hallarta zabbukan na kananan hukumomi ba.Jam'iyyar tace abinda ke zaman wajibi na ta shiga a dama da ita shine na ganin an sako jagoranta wanda Kotun Duniya dake hukunta manyan laifukan yaki ke tuhumarsa da laifukan cin zarafin bil Adama.

Mawallafi: Abdourahmane Hassane
Edita: Yahouza Sadissou Madobi

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani