Jam′iyyar FPÖ a Austriya na cin mutuncin musulmi a yakinta na neman zabe. | Siyasa | DW | 15.01.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Jam'iyyar FPÖ a Austriya na cin mutuncin musulmi a yakinta na neman zabe.

Jam'iyyar FPÖ mai tsattsauran ra'ayin kyamar baki a Austriya na cin mutuncin musulmi a yakinta na neman zabe.

default

Susanne Winter

Bisa ga dukkan alamu, jami'an siyasar jam'iyyar FPÖ mai zazzafan ra'ayin mazan jiya a kasar Austriya ba su shayin cin mutuncin mutane a yake-yakensu na neman zabe. Wannan maganar musamman ta shafi baki, galibi musulmi kamar yadda ya faru a baya-bayan nan inda suke rura wutar adawa da musulunci. A halin yanzu haka wani mai daukaka kara da sunan gwamnati a garin Graz dake kasar ta Austriya ya gabatar da matakan bincike akan laifin neman rura wutar rikici tsakanin jama'a akan wata jami'ar siyasar jam'iyyar ta FPÖ, wadda a yakinta na neman zabe ta rika maganganu na batanci akan mazon Allah Mai tsira da aminci. Ahamad tijani Lawal na da rahoto akan martanin da ake mayarwa dangane da wannan badakala. A ranar lahadi mai zuwa ne za a gudanar da zaben kananan hukumomi a garin Graz, wanda shi ne na biyu wajen girma a kasar Austriya, kuma dukkan jam'iyyun siyasar kasar na gwagwarmayar neman rinjayen kuri'u, abin da ya hada har da jam'iyyar FPÖ mai tsattsauran ra'ayin kyamar baki. Ita wannan jam'iyyar tana amfani da duk wani abin da take ganin wata dama ce a gare ta wajen neman kuri'u. A sakamakon haka take yayata manufofin kyamar baki da adawa da musulunci. Babbar 'yar takarar jam'iyyar a Graz mai suna Susanne Winter tayi imanin cewar ta san dabarun shawo kan jama'a don ba ta goyan baya, kuma abin mamaki mutane kimanin dubu uku da suka halarci dandalin yakinta na neman zabe suka rika yi mata tafi da guda lokacin da take cewar wai garin Graz na fama da bala'in tuttudowar musulmi kamar ambaliyar tsunami sannan ta kara da maganganu na batanci ga mazon Allah Mai tsira da amince, wai a matsayinsa na mai shekaru 50 da haifuwa ya auri wata yarinya 'yar shekara shida. Wannan lafazin da aka ji daga bakinta ya jefa abokan adawarta cikin hali na dimuwa da mamaki. Amma Susanne Winter ba ta dadara ba tana mai kalubalantar illahirin musulmi da laifuka na cin zarafin yara a cikin hira da wata jarida tayi da ita. Ta ce wai wajibi ne a fatattaki musulmi daga nahiyar Turai har sai sun koma ketare tekun bahar rum. Ire-iren wadannan furuce-furuce, ba kome ba ne illa wata manufa ta rura wutar rikici tsakanin jama'a, a cewar babban lauya mai daukaka kara da sunan gwamnati a garin Graz ya kuma gabatar da bincike kanta. An ji daga kakakinsa yana mai cewar: "Ana tuhumarta ne da lafin rura wutar rikici a zukatan jama'a, wanda laifi ne da za a iya yanke wa mutum hukuncin daurin shekaru biyu a gidan kurkuku." Shi kuwa shugaban jam'iyyar ta ta FPÖ Heinz-Christian Strache ba ta goyan baya yayi, inda yake cewar: "Shin dukkan abin da ta fada daidai ne ko ba daidai ba? Muna iya cewar tayi magana mai tsaurin gaske. Amma fa ba zan iya hana wa mutum fadar ra'ayinsa ba." Tuni dai sauran jam'iyyun siyasa da kungiyoyin addinai na kasar Austriya suka fito fili suna masu Allah Waddai da wannan furici da ya fito daga bakin Susanne Winter. Shugaban gwamnatin kasar Alfred Gusenbauer ya ce ba wani dake da 'yancin cin mutunci da zarafin wasu saboda banbancin addininsu. A cikin hira da aka yi da ita wata jami'ar siyasar kasar Austriya 'yar usulin Turkiyya Akgün ta bayyana bakin cikinta game da yadda ake shigar da manufofi na kabilanci da kyamar baki a harkoki na siyasa a kasar. "Akgün ta ce:Ire-iren wadannan jam'iyyu masu tsattsaran ra'ayin kyamar baki, a kodayaushe suna bakin kokarinsu wajen neman mutumin da zasu dora masa alhakin halin da ake ciki domin neman goyan-baya daga jama'ar, musamman a lokutan zabe. Abu mafi alheri shi ne a yi watsi dasu saboda ba su da wata martaba, sai dai kwai a rika wulakanta su." 'Yan jam'iyyar the Greens a kasar Austriya din sun yi kira da a kawo karshen wannan mataki na adawa da musulmi da jam'iyyar FPÖ take yi. Kakakin jam'iyyar ta the Greens akan manufofin tsaro Peter Pilz ya ce FPÖ na amfani ne da hali na dardar da mutane ke ciki don cusa musu akidar kyamar baki. Wajibi ne a tinkari matsalar tare da hankali da basira. Za a dai ci gaba da yakin neman zabr a Graz ta Austriya har ya zuwa ranar lahadi, kuma sai bayan haka ne za a kawar da allunan jam'iyyar ta FPÖ masu dauke da lafuzzan kyamar baki da adawa da musulmi daga titunan garin.