1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 111 da samar da jam'iyyar ANC

Binta Aliyu Zurmi
January 8, 2023

A yau Lahadi jam'iyyar ANC mai mulki a kasar Afirka ta Kudu ta cika shekaru 111 da kafuwa, an gudanar da gagarumin biki a cibiyar jam'iyyar da ke lardin Free State inda aka samar da jam'iyyar a shekarar 1921.

https://p.dw.com/p/4LsgV
Südafrika | ANC Präsident Cyril Ramaphosa
Hoto: Denis Farrell/AP Photo/picture alliance

Shugaba Cyril Ramaphosa da aka sake zaban shi a matsayin jagoran jam'iyyar a watan Disamba bara ya gabatar da jawabi ga dimbin 'ya'yan jam'iyyar da ma magoya bayanta a kan irin yadda suke shirin tunkarar kalubalen da kasar ke fuskanta a yanzu.

Jam'iyyar ANC ita ce jam'iyya mafi dadewa a kasar wacce ta faro daga fafutukar kawar da mulkin mallaka na tsiraru fararen fata ya zuwa mulkin dimukuradiyya.

Sai dai wannan bikin na zuwa ne a daidai lokacin da tagomashin jam'iyyar ke dusasashewa a idon al'ummar kasar bisa wasu dalilai da suka hada da zargin cin hanci da rashawa da ake yi wa wasu yayanta dama tsadar rayuwa da al'ummar kasar ke fama da shi.

Marigayi Nelson Mandela ya kasance zababen shugaban kasa na farko a jam'iyyar ta African National Congress bayan kwashe shekaru 27 a gidan yari da shi da wasu yayan jam'iyyar.