Jam′iyyar AfD ta kayar da CDU ta Merkel | Labarai | DW | 04.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jam'iyyar AfD ta kayar da CDU ta Merkel

Sakamakon farko na zaben 'yan majalisar dokoki a jihar Mecklenburg-Vorpommern ta Jamus na nuna cewar jam'iyyar CDU ta shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta sha kaye a hannun jam'iyyar da ke kyamar da baki wato AfD.

A bisa alkaluman kididdiga da gidan Talabijin na ZDF ya fitar, Jam'iyyar Afd mai kyamar baki ta sami kashi 21.5 cikin dari na kuri'un da aka kada.Hakan na nufin cewar a karon farko jam'iyyar za ta shiga majalisar dokokin jihar ta arewa maso gabashin Jamus. Da ma dai tana da wakilai a majalisun dokoki a jihohi takwas na tarayyar Jamus.Akwai kuma yiwuwar cewar jam'iyyar na iya samun damar shiga majalisar tarayya ta kasa a babban zabe da za'a yi a shekara mai zuwa.

A waje guda dai Jam'iyyar CDU ta shugabar gwamnati Angela Merkel ta sami kashi 20 ne cikin dari na kuri'un da aka kada a zaben na yau, wanda ke nufin cewar ta fado zuwa matsayi na uku a jerin jam'iyyun da ke da karfi a jihar ta Mecklenburg Vorpommern . Mutane kimanin miliyan daya da dubu dari uku ne suka kada kuri'a zaben.