JAMIYYAR ADAWA TA ZIMBABWE TA KAI KOKENTA GA KUNGIYYAR EU. | Siyasa | DW | 29.01.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

JAMIYYAR ADAWA TA ZIMBABWE TA KAI KOKENTA GA KUNGIYYAR EU.

Shwagabannin jamiyyar adawa ta MDC dake kasar Zimbabwe sunyi kira na musanman ga kungiyyar tarayyar Turai,wato Eu data yiwa Allah tayiwa annabi ta kara kakabawa gwamnatin shugaba Robert Mugabe takunkumi.
Shuwagabannin jamiyyar ta MDC tayi wannan kiran ne ga kungiyyar ta Eu a wani taro daya gudana a tsakanin su a makon daya gabata bisa dalilin haramci na gwamnatin da kuma ire iren abubuwan da take tafkawa a halin yanzu wadanda suka saba da mulkin dimokradiyya. Shugaban tawagar shuwagabannin na jamiyyar ta MDC mai suna Sibanda yaci gaba da cewa bayan kara tabbatar da takunkumin da kungiyyar ta Eu ta sawa kasar jamiyyar tasu na kuma son kara fada dasu dasu fi nada yawa.
Sibanda ya kara da cewa ta hanyar yin haka ne kawai kasashe da kungiyoyi masu fada aji a duniya zasu takurawa shugaba Mugabe wajen dawowa izuwa teburin sulhu da jamiyyun adawar kasar don tattauna yadda za,a tsamo kasar daga cikin halin kaka ni kayi data tsinci kanta a ciki.
A takaicen takaicewa inji Mr Sibanda Jamiyyar ta MDC na son ganin shugaba Mugabe ya kyale an gudanar da zabe mai tsabta ne a cikin fadin kasar baki daya,domin a cewar sa gwamnatin ta mugabe ba halattacciyar gwamnati bace domin ta gudanar da magudi ne cikin zaben daya bata nasarar cafke kujera mai alfarma ta kasar wato ta shugaban kasa.
Shugaban adawar ta majalisar dokokin kasar kuma mataimakin shugaban jamiyyar ta MDC ya kara kira ga kungiyyar ta Eu data bawa kwamitin sulhu na mdd shawara na duba yiwuwar hanyoyin daukar matakan soji kann gwamnatin ta Mugabe don ganin kwalliya ta biya kudin sabulu.
A kuwa ta bakin kakakin wasu kungiyoyi masu zaman kansu kusan talatin,Brian Kagoro cewa yayi akwai bukatar matsawa gwamnatin Mugabe daga bangaren kasashen ketare don fitar da mutanen kasar daga cikin kangi na wahala da fatara da suke fama da ita shekara da shekaru. A baya dai kungiyyar ta Eu ta sawa shugaba Mugabe da wasu na hannun daman sa 72 takunkumi na kada su shiga cikin kasashe mambobin ta tare da rufe ma,ajiyar su dake bankuna a kasashen yayanta,a karshe kuma ta hana sayarwa da kasar makamai,wanda har ya zuwa yanzu dokar na aiki baza kuma ta kare ba har sai nan da 20 ga watan fabarairun wan nan shekara da muke ciki.
A kuma dai dai lokacin da ake tsamnanin karewar ta a dai dai lokacin ne kuma ake gudanar da shirye shiryen kara tabbatar dasu a hannu daya kuma yan adawar kasar ta Zimbabwe ke muradin ganin an kara wasu bayan nada.
Shugaba Mugabe ya dai kasance yana mulkin kasar ta Zimbabwe ne a tun lokacin da kasar ta samu yancin kanta a shekara ta1980 daga kasar Biritaniya,zabe kuma na baya bayan nan da aka gudanar a shekara ta 2002 wanda ya kara bawa Mugabe damar ci gaba da mulkin kasar ya samu kakkausar suka daga bangfarori daban daban na kungiyoyi masu zaman kasu da kuma kasashe masu fadfa aji na duniya,da cewa an tafka magudi ne a cikin sa.