Jam′iyya mai mulki a Turkiya ta rasa rinjaye. | Labarai | DW | 07.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jam'iyya mai mulki a Turkiya ta rasa rinjaye.

Sakamakon zaben 'yan majalisun dokokin Turkiya ya bada jam'iyya mai mulki ta AKP kan gaba da yawan kujeru, sai dai kuma ta rasa rinjayen da take da shi a majalisa.

A wata sanarwa da aka bayar ta gidan talbijin din kasar bayan da aka kidaya fiye da kashi 70 cikin 100 na yawan kuri'un da aka kada, jam'iyya mai mulki ce ke kan gaba da kashi 43 cikin 100 na yawan kuri'un da aka kada, abun da ya bata 'yan majalisun dokoki 267 daga cikin 550 wanda hakan zai tilasta kafa gwamnatin hadaka a wannan kasa da jam'iyya mai mulki ke da rinjaye tun shekaru 13 da suka gabata. Jam'iyar Kurdawa ce ta ADH ce dai ta taka rawar gani da fiye da kashi 10 cikin 100 na yawan kuri'un, abun da yabata 'yan majalisu guda 70. Jam'iyar 'yan gurguzu ta CHP ce tazo ta biyu da Kujeru 124 yayin da jam'iyar Action National ta MHP ta samu kujeru 85.