Jam′iyun adawa a Najeriya sun hade da juna | Siyasa | DW | 07.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Jam'iyun adawa a Najeriya sun hade da juna

Bayan kai da komo na tsawon shekaru masu yawa manyan jam'iyun adawa sun cimma yarjejeniyar hadewa wuri guda da nufin kalubalantar jam'iyar PDP dake mulki

Kasa da tsawon hawoyi 24 da bayyana hadewar su zuwa jam'iyyar APC, masu ruwa da tsaki da batun siyasar tarrayar Najeriya na ci gaba da maida martani ga matakin da daga dukkan alamu ya kama hanyar bude sabon babi ga siyasar kasar.

Sun dai zo daga yan gurguzu da masu ra'ayi irin na yan mazan jiya.Sun kuma share sama da shekaru suna fafutuka ba nasara, kafin hadewar tasu wuri guda da nufin haihuwar jam'iyyar adawa mafi girma a cikin tarihin siyasar kasar ta Najeriya . Hadewar manyan jamiyyun adawar kasar na CPC da CAN da ANPP da kuma APGA zuwa APC dai na zaman wani sabon yunkuri a bangaren adawar kasar ta Najeriya da suka ce mafita kadai a kokarin su na kawo karshen babakeren jamiyyar PDP da ta share shekaru 14 tana cin karenta babu babbaka na zaman hada karfi da tunanin su wuri guda.

Nigeria Wahlen Muhammadu Buhari Oppositionsparteiführer ANPP

Janar(mai ritaya) Muhammadu Buhari

Abun da kuma a cewar senata kabiru gaya dake zaman daya daga cikin yan kwamitin gammayar jamiyyun ya kaisu ga mantawa da banbance bancen su na baya domin kafa sabuwar nigeriar da kowa zaiyi alfahari da ita

Sa Najeriya a gaba ko kuma yaudarar kai dai ya zuwa yanzu yan adawar kasar ne ke rike da gwamnoni 12 cikin 36 da kasar ke takama dasu, sannan kuma da kusan kaso 35 cikin dari na yan majalisun tarrayar kasar. Abun da kuma ya sa wasu ke kallon kafa APC a matsayin wani bude sabon babi ga siyasar kasar ta Nigeria. To sai dai kuma a cewar Hon. Bala Kaoje dake zaman ma'ajin jamiyyar PDP na kasa ba anan take ba wai an danne bodari aka.

Nigeria Jonathan Goodluck

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan na jam'iyar PDP

Suddabaru ga siyasa ko kuma kama hanyar fito na fito da haihuwar sabuwar jam'iyyar na iya kaiwa ga sake dawo da siyasar bautar al'umma maimakon uban gida da yaronsa da ta mamaye harkokin kasar a yanzu. Abun da kuma a cewar Garba Umar Kari dake zaman masanin harkokin zamantakewa a jami'ar Abuja ke iya jefa sabon fatan sauyi a cikin zukatan alumar kasar.

Abun jira a gani dai na zaman hadin kan yan adawar dama hadiyar burin mulkin nasu domin iya yin tasiri ga makomar siyasar tarrayar Najeriyar.

Mawallafi: Ubale Musa

Edita: Umarau Aliyu

Sauti da bidiyo akan labarin